Labarai

Hajjin 2023 Miliyan 3 kowane maniyyaci zai biya a bana —NAHCON

 

Hukumar kula da aikin hajji ta kasa (NAHCON) ta bai wa hukumomi, rassa-rassa da suke da ruwa da tsaki a harkar biyan kudin hajji tare da hukumomin da ke kula da jin dadin Alhazai na jihohi wa’adin zuwa ranar Juma’a su tura dukkanin kudaden kujerar aikin Hajjin 2023.

Shugaban hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan, shi ne ya bayar da wannan wa’adin a jiya sa’ilin wata ganawa da manyan jami’an da ke kula da hukumomin kula da jin dadin Alhazai da sauran wadanda lamarin ya shafa da ya gudana a Hajj House, Abuja.

A cewar sanarwar da mataimakiyar daraktan sashin yada labarai na hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce, zaman ya cimma muhimman batutuwa da suka dabaibaye shigar da kudaden kujerar aikin Hajjin ta hanyar da daidaitawa da shigar da adadin maniyyatan da suka cancanta suka dace da za su samu tafiya daga Nijeriya.

A cewar sanarwar ta hanyar hakikance adadin ne za a rattaba hannun yarjejeniya da jiragen da za su yi jigilar.

Hassan ya ce, hukumar za ta yi amfani ne kawai da adadin kudin mutanen da aka shigar zuwa asusun da aka ware daga ranar Juma’a kuma da adadin ne za a sanya hannun yarjejeniya da kamfanonin jiragen saman da za su yi jigilar zuwa Saudiyya Arabiyya.

Akan hakan, duk kudin da bai shiga ba kafin ranar Juma’a ba zai samu tafiya aikin hajji na 2023.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button