RANA ƊAYA

0
207

📚4️⃣
Page 6

Biye mata. Ta je ta yi ta zama, amma fa ba zan sake ta ba, lokaci bai yi ba”Ya kai awa biyu kafin ya ji shigowar Nafisa, don hauka gidan a bude ta barshi, karar talabijin da ta ji daga dakinshi shine ya sa ta nufi dakin cikin sauri. Gabanta ya fadi da ganinshi kwance, duk da tana cikin damuwa kuma ta kosa ya dawo don a yi wadda za a yi,amma sai da ta tsorata da ganinshi. Ta ce, “Au ka iso kenan?”Ya ce,

“Ina ki ka je?”Gabanta ya fadi ganin yanda ya murtuke fuska, amma da ta tuna inda ta je cikin gadara da son ya san tasan yana neman wata ta ce, “Gidan su Zinatu na je”Ya dube ta da sauri,Wace ce kuma Zinatu? Mene ne alakarku da har za ki je gurinta ki kwashe sama da awa biyu ba tare da izinina ba? Kuma ki bar min gida a bude?” Nafisa ta ce,

“Ai gani na yi don na je gurin Zinatu ai kara na maka, kodayake na fada mata cewa, mu hudu ne duk da ta ce ka mata alkawarin sakin daya daga cikinmu don ka maye gurbi da ita. Sai dai ina neman alfarma a sake ni, don bana son a jona ni da cutar zamani Kan Shatima ya kulle, sam bai fahimci me Nafisa ke son fada mishi ba, illa dai ya fi tunanin borin kunya take son yi

“Zan fi son ki fada min gaskiya fiye da wannan borin kunyar. Abin da kawai nike son sani, inda ki ka je”Murmushi tayi Ta ce,Baban Ashraf kenan, ban ce kana borin kunya ba sai ni? To bari dai in fito maka baro-baro gurin karuwarka na je Zinatu!”

Shatima ya daga hannu zai tsinke Nafisa da mari, sai muryar Hajiya Kaka ta zo masa,” Wannan ba dabi,ar gidanmu ba ce! ba a dukan mace!’Ya kankame hannunshi tam jikinshi har Bari yake yi, ya sa kai zai fita yana jin tana fadin,”‘Da ka da ke ni, Allah da ka daki auranka”Shatima ya fada mota a fusace, ya fige ta tamkar zai tashi sama, amma sai motar ta mutu kafin ya kai bakin get, ya san cewa batir din yayi-sanyi tunda ba da ita ya je Kaduna ba, kuma ga -shi yanayin sanyi ake ciki. Ya fito ya bar motar nan ya fita ba tare da ya san ina za shi ba.Yayi tafia mai nisa kafin ya zauna bakin wani masallaci; munane suna ta alwala. Shi ma ya yi,

sannan ya bi sahun sallar. Yana zaune bayan an idar, tunani yake yi, wai su mata har abada suna da lissafi kuwa? Ko dai sun hada baki ne don su tozarta shi su uku? Shi ya sa yana son Aliya, yana kuma girmama lamarinta, ita ce har zuwa yau daga auransu ba za ya tuna wani abu da ta yi masa wanda zai Bata masa rai Abin da zai fi kawai gara ya hada su su ukun ya sake su, inyaso ya yi zamansa da Aliya. Wace ce Zinatu? Wai kuma karuwarsa? Nafisa tana hauka ne ta ke danganta shi da wannan laifin? Yana da mata har hudu me zai burge shi da wata matar waje? To ko Salma ita ma ta ji wannan zancen ne? Haka ya yi ta tufka da warwara har aka kira la ‘asar ya yi.

Ya jima yana addu’o’insa, sannan ya ji zuciyarshi ta dan yi sanyi. Lallai lamarin mata sai addu’a, amma ya daina saka kanshi cikin damuwa, duk wadda ta gaji to zata iya tafiya gidansu.

Abin da ya faru, Nafisa tunda ta ji labarin

Zinatu shi ke nan ta shiga bin diddigi har sai data gano gidan su Zinatu, wanda yake a cikin layin. Zinatu da yayarta duk suna zaman kansu ne, Nafisa ta kama hanya ta nufi gidan nasu wai za ta yi wa Zinatu kashedi duk kuwa da shawarar da Maman Nana ta bata na cewa, kar ta je. Ta samu Zinatu tana cin taliyar indomi, Nafisa tana ganinta ta gane cewa ita ce Zinatu, saboda surarta da ake bada labari. Nafisa ta ce,Ke ce Zinatu ko?”Zinatu ta ce,

“Nice,ke ce Maman Ashraf?”- Nafiza ta zaro ido, Zinatu ta ce,Kina mamakin yanda aka yi na sanki ne?”Ta nuna mata kujera,

“Zauna mu yi magana, kin san an ce shirin zaune ya fi na tsaye Nafisa ta ce,

“Ban zo zama ba, zuwa na yi in ja kunnenki ki fita hanyar mijina”

Zinatu ta Ce,Tofa! Ki ce da babbar magana ki ka zo. To amma kin makara tunda har ki ka bari na soma sonsa, sannan shi ne yafi dacewa da ki ja masa kunne, don shine ya gani ya taya”.Ta mike tsaye tana juyi gaban Nafisar,Kalle ni sosai, ba ni da makusa. Ki bari in auri kyakkyawan mijinki, ina sonsa da yawa”.Nafisa ta ce,Ki aure shi ta ina? Ai mu hudu ne a gurinsa, kin ga kenan ba ki da sauran gurin shiga tunda mu din musulmi ne”

Zinatu ta boye mamakinta, wai su hudu ne, ko dai ta ce haka ne don ta sa ta rabu da shi?Ta dubi Natsa,Ya yi min alkawarin sakin daya don ya maye gurbi da ni. Zai fi kyau ki rage kishi don kishi da ni babu dadì. Duk gidan da na shiga nice mandiya, kin san Mandiya?” Bata jira amsa ba, ta ce, “Ina nufin isasshiya”Nafisa ta ce,Insha Allah ba za ki shigo cikinmu ba, ki je can ki nemi watsattsu irinki”Zinatu ta yi dariya In kin je ki tambayi mijinki sau nawa muka watse da shi? Sannan ki fita, ina da ‘yan daba, waya kawai zan musu sai sun yaga ki”Nafisa ta ce,

“Insha Allahu mijina ya fi karfinki”. Ta fice da sauri ganin Zinatu tana danna waya.Tana jiyo dariyar Zinatun tana fadin,Karamar kwaruwa”.*Shine tana zuwa ta amu Shatiman ya zo.

Bayan sun yi wannan sa’insar ya fita, ta ce,

“Aiko na rantse ba zan ji wannan bakin cikin ni daya ba, dole sai na fada ma sauran matanshi nima, kowacce ta dandana Ta soma laluben layin Aliya tana fadin,

“Kila ma don ita ne ya dawo da safen nan, harni zai wa alaye wai bai sonta?”Aliya ta daga cikin sauri da mamakin kiran Nafisa gare ta, domin ba ta kiranta a waya, ba ta yi zaton Nafisar tana da lambarta ba. Suka gaisa à takaice, Nafisa ta ce, “Maman Abulkhairi

Leave a Reply