RIBAR BOKO

0
63

 

“Ta farfaɗo.” Jin wannan kalmar ya sa na tabbatar har yanzu ina raye. Na zabura zan ruga na ji an riƙe ni.
“Don Allah ku ƙyale ni! Na fi son mutuwa fiye da rayuwa, da kaina na faɗa ruwa don na mutu.”
Likita aka kira ya yi mini allura. Bayan na farka Malam Haladu mai lambu, wanda ya tsince ni a bakin rafi, ya kai ni gidan Hajiya Jummai mai taimaka wa maɓukata.

Da ƙyar na iya ba su labarina.

Sunana Hauwa’u Ja’o, na taso a gaban iyayena cikin rugarmu ta Fulani. Kasancewata auta ya sa na samu gatan da sauran ‘yan’uwana ba su samu ba.
Lokacin da nake ƙarama ina bin mahaifina kiwo, a nan nake ganin yara ‘yan makarantar Hayin Kogi,
Hakan yana matuƙar ba ni sha’awa, nakan tsaya kallon su wasu lokutan kuma har bakin tagar ajin nake zuwa na saurari karatun da ake koya masu.
Watarana malamin aji ya yi tambaya kowa ya kasa amsawa, daga bakin taga na ba da amsar, hakan ya sa malamin jin daɗi ya ce in jira shi ya fito, na ruga wurin mahaifina na ɓuya a bayansa. Ko da ya iso hannu ya miƙa suka gaisa, ya tambaye shi ya alaƙata take da shi? Ya ce shi ne mahaifina.
Malamin ya sanar masa ina da saurin fahimtar karatu ya shawarce shi da ya sanya ni a makaranta.
Jin haka ya sa ni fitowa fuskata ɗauke da murmushi, ina kwaɗayin shiga makaranta, mahaifina ya sanar masa ‘ya’yansu ba sa yin karatun boko.
A nan malamin ya yi ƙoƙarin nuna masa muhimmancin karatun boko a cikin al’umma, musamman ga ‘ya mace.

Jikinsa ya yi sanyi, ya amince da maganar malamin da alƙawarin zai sanya ni.
Malamin ya ji daɗin fahimtarsa da ya yi, ya ce zai saya mini dukkan abin buƙata na makaranta ina iya fara zuwa gobe.
Godiya sosai Babana ya yi masa tare da alƙawarin washegari zan fara zuwa.
Wannan shi ne silar shigata makaranta, wanda a tarihin rugarmu da zuri’armu ni ce farkon wadda ta fara karatun boko.
Hakan ba ƙaramin surutu ya janyo wa mahaifina ba cewar zan lalace, danginmu za mu zama abin kwatance da nuna ƙyamar haɗa zuri’a da mu.
Mahaifina ya toshe kunnuwansa a kan duk wasu ƙananan maganganun da ake yi.

Isyaku ƙanin mahaifina ya fi kowa ɗaukar zafi, domin akwai alƙawarin aure tsakanina da ɗansa Ya’u, lokacin da na fara tasawa ya tuntube shi a kan zancen auren sai ya nuna mashi ina karatu ba yanzu ba, ya yi fushi sosai! Tun daga nan bai sake yin maganar ba.
Haka na cigaba da karatu a ƙarƙashin kulawar mahaifina, har Allah ya sa na shiga shekarar ƙarshe a sakandare cike da burin zuwa matakin gaba.
Watarana mahaifina ya kwanta rashin lafiya, ashe ciwon ajali ne.
Cikin dare Allah ya yi masa rasuwa. Babu shakka, mutuwar mahaifin nawa ta girgiza rugarmu sosai, domin ya kasance mutumin kirki ne ƙwarai. Allah cikin ikonsa, mutuwar mahaifina sai ta yi sanadin aurena bayan kwana bakwai da barinsa duniya.
Lokacin da labarin ya iso gare ni kusan zaucewa na yi, zafi biyu a lokaci guda, mutuwar mahaifina da kuma rushewar karatuna.
Bayan sati ɗaya na tare a gidan mijina wanda a haife ya haife ni, domin ɗansa na uku shi ne sa’ana.
Da farko na ƙi zama, kullum cikin gudu nake ana mayar da ni. Wani gudu da na yi ya zama na ƙarshe, mahaifiyata da yayyena suka yi min dukan tsiya sai da na yi jinya, daga nan na sanya wa zuciyata haƙuri, na rungumi aurena a matsayin ƙaddarata, har Allah ya sa na samu juna biyu kullum cikin ciwon laulayi.
Na roƙi Ya’u ya bar ni in je asibiti, Sam! Ya ƙi. Amma duk ‘yan’uwana da mahaifiyata babu wanda ya goya min baya, cewarsu karatun da na yi ya ɓata min tarbiyya, duk rugarmu babu wanda ya taɓa zuwa asibiti domin wata cuta ko haihuwa, don haka a kaina ba za a fara ba.
Abin da suka sani suka gada a shiga daji a sassako magani a sha a warke.
Dole na haƙura har lokacin haihuwata ya yi, cikin dare na farka da azababbiyar naƙuda, an kira ungozoma har tsawon kwana uku ina shan azaba, duk da haka ba su tausaya suka kai ni asibiti ba. A rana ta huɗu na haihu ɗan bai zo da rai ba.
Ya’u ya fi nuna damuwarsa kan rashin ɗan fiye da halin da na shiga.
Bayan wani lokaci na fahimci ba na iya riƙe fitsari, lemarshi kawai nake gani ba tare da na san lokacin zubowarshi ba.
Na sanar da su halin da nake ciki, sun yi duk wasu dabarun da za su yi abu ya ci tura, dole suka amince muka je asibiti. Mun sha wulaƙanci kafin aka karɓe ni, likita ya shaida masu na gamu da cutar yoyon fitsari, don haka sai an yi min aiki, da ƙyar Ya’u ya amince ya biya kuɗin.
Bayan wata uku da yi min aiki, yoyon fitsarin ya sake dawowa, muka koma asibiti suka ce sai an sake yi mini sabon aiki, Ya’u ya yi ta sababi shi ba zai sake ɓarnatar da dukiyarshi ba, tunda an yi na farko bai yi ba babu tabbacin idan an sake yin aikin zan warke.
Nakan yi kuka, musamman idan na shiga mutane na ga suna kyara ta.
Ya’u ya ƙaurace wa duk wata alaƙar da za ta sada mu ko da a hanya ce, idan ko muka haɗu bisa kuskure, ya dinga toshe hanci haɗi da tofar da yawu ke nan.
Ina cikin wannan yanayin ya ce ba zai iya cigaba da zama da ni ba, haka ya sake ni saki uku.
Ƙyama da tsangwama har cikin gidanmu ana nuna min, idan na je wuri sai a fara toshe hanci daga nan kowa ya watse ko a kore ni daga wurin. Wannan dalilin ya sa aka ware min ɗaki a can gefe.
Da zaman ya ishe ni na yanke shawarar komawa makaranta, babu wanda ya yi yunƙurin hana ni.
Rana ta biyu da komawata makaranta, abokan karatuna suka fara nuna min ƙyama, ƙarshe ficewa suka yi daga ajin, a cewarsu, wai warin da nake yi yana damun su.
Shugaban makarantar da kanshi ya kira ni zuwa ofishinsa, ya shaida min ɗalibai sun koka kan warin da nake yi, don haka an dakatar da ni har sai na samu lafiya. Na yi kuka kamar raina zai fita, haka na haƙura da karatun.
Watarana ƙishi ya dame ni, ruwan ɗakina ya ƙare sai na nufi ɗakin mahaifiyata da nufin in samo a randarta, ai kuwa faɗa ta hau da shi, wai don me zan taɓa mata randa bayan ƙazantar da ke jikina? Zuciyata ta yi ɗaci, fizge ni na nufi rafi cikin fushi.
Na tarar da ‘yammata masu ɗiban ruwa, dariya suka riƙa yi min haɗi da toshe hanci, suna kira na ‘yar bokon da babu riba.
Baƙin ciki ya yi min yawa, na yanke hukuncin faɗawa ruwa kowa ya huta, tun da rayuwata ba ta da amfani. Mahaifiyata da sauran mutane sun tsane ni saboda lalurar da nake fama da ita.
Hajiya Jummai ta share ƙwallarta ta ce, “Duk wannan tashin hankalin a kan silar ɗa namiji ko?
Da yardar Allah kukanki ya zo ƙarshe, na yi miki alƙawarin nema maki lafiya, tare da ingantaccen ilimin da kike buri.
Sannan kar ki sake yunƙurin kashe kanki, hakan ba mafita ba ce.”
Bayan shuɗewar shekaru na cim ma burina na yin karatu, ban koma rugarmu ba, har sai da na zama cikakkiyar likitar mata, tare da taimakon Hajiya Jummai.
Ranar da na dira rugarmu sun cika da mamakin ganin manyan motocin da ba su taɓa gani ba a ƙofar gidanmu.
Mamakin su ya ƙaru lokacin da suka gan ni, duk tunanin su na mutu a ruwa.
Na yi wa su Hajiya Jummai da sauran ‘yan tawagar ƙungiyarta jagora har cikin ɗakin mahaifiyata, wacce take jinya tun lokacin da aka sanar mata na faɗa a rafi, ko gawata babu.
Da ƙyar ta iya ɗago kai, kallo na take yi cike da mamakin wannan Hauwa’un da ke gabanta ta daban ce, wayayyya ce ‘yar gayu, ga alamu hutu ya ratsa jikinta. Ta cika da mamakin gani na a raye, ta yi kuka haɗe da nadama ta gode wa Allah da ya sake sada ta da ni.
Na gabatar da su Hajiya Jummai da tawagarta, na yi bayanin irin taimakon da suka yi min, tun daga ceto na daga mutuwa har zuwa neman lafiya tare da ingantaccen ilimi.
Ta rasa kalmar da za ta gode masu, sai faɗin na tuba, sun yi mata nasiha a bisa kuskuren da ta aikata a matsayinta na uwa.
Na wallafa labarina a yanar gizo wanda a dalilin haka ƙungiya mai zaman kanta ta NGO, suka ziyarci rugarmu tare da gina makaranta , yanzu ilimi ya yawaita kuma suna zuwa asibiti musamman mata masu juna biyu, ni ce babbar likitar mata a asibitin garin.
Na zama tauraruwa abar koyi ga mutanen rugarmu, da sauran al’umma.
Na taimakawa tsohon mijina Ya’u a ƙarkashin ƙungiyata, ta k’alubalen mata wanda ke a kafar Intanet, mai haɗin gwiwa da lauyoyi da ƙungiyar kare haƙƙin ƙananun yara.
Na samu nasarar yi wa ɗiyarsa mai ƙarancin shekaru aikin yoyon fitsarin da ta gamu da shi sanadiyyar fyaɗen da aka yi mata, an gurfanar da wanda ya yi fyaɗen a kotu domin kwato wa yarinyar hakƙinta, sai a lokacin Ya’u ya fahimci Ribar Boko.

Karshe!

Leave a Reply