Sadiya Umar Farouq Bazamfariyar ƙwarai ce – Gwamna Matawalle

0
210
    Gwamna Matawalle tare da Minista Sadiya Umar Farouq a wajen taron

 

Gwamna Bello Muhammed Matawall na Jihar Zamfara ya bayyana Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Uma Farou,a matsayin nagatartacciyar ‘yar jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne kwanan nan a wajen ƙaddamar da shirin ba da tallafin kuɗi ga mabuƙata, a turance ‘Cash Grant for Vulnerable Groups’ wanda aka yi a zauren majalisa na Gidan Gwamnati a Gusau.

Gwamna Matawalle ya lissafa alfanun da jihar sa ta samu daga Shirye-Shiryen Inganta Rayuwar Jama’ar Ƙasa (NSIPs), sannan ya yaba wa Ministar da Shugaba Muhammadu Buhar saboda ƙoƙarin su na rage fatara da yunwa a Nijeriya.

Ya ce: “Ministar ta na ta ƙoƙarin tabbatar da cewa ita nagartacciyar ‘ya ce daga jihar mu. Hakan a bayyane ya ke idan an yi la’akari da jerin shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya na agajin jama’a wanda ma’aikatar ta ke aiwatarwa, waɗanda jihar mu ta amfana ƙwarai da gaske daga gare su.

“Haka kuma mun ga haka ta wajen ƙaunar da ta ke nuna wa wannan gwamnatin a kowane lokaci.

“Na fahimci cewa ministar ta zo Jihar Zamfara ne domin ta rarraba kayan abinci da sauran kayayyaki ga ‘yan gudun hijira, kuma ta ƙaddamar da Shirin Ba Da Tallafin Kuɗi ga Mabuƙata, kuma ta raba takardun kama aiki ga ma’aikata ‘yan sa ido masu zaman kan su da aka ɗauka, sannan kuma ta ba da rance maras ruwa ga manoma da mata ‘yan kasuwa.

“Waɗannan abubuwan hoɓɓasa da ake yi wasu muhimman matakai ne da ake ɗauka domin a rage fatara tare da ƙarfafa wa mutanen mu gwiwa ta fuskar tattalin arziki. Halin ƙunci da ake ciki a ƙasar nan ya na buƙatar gwamnatoci a kowane mataki su dage su yi aiki wurjanjan. Wannan ƙoƙarin ya na zuwa ne a matsayin ɗori a kan ƙoƙarin da gwamnatin wannan jihar ke yi ta fuskoki da dama
domin ta sauƙaƙa wa jama’ar wannan jihar.”

A nata jawabin, Minista Sadiya Umar Farouq ta bayyana cewa ma’aikatar ta za ta raba agajin kuɗi ga mabuƙata 4,728 da ke Ƙananan Hukumomi 14 da ke faɗin jihar, yayin da an tantance tare da lissafa mutum 4,616 da za su ci moriyar lamunin Shirin Tallafin Kasuwanci na Gwamnati (wato GEEP) wanda babu ruwa a cikin sa, wanda ya kama daga N50,000 zuwa N300,000.

Ministar ta kuma ƙaddamar da Shirin Faɗakarwa na Ƙasa kan Shirin Ciyar Da Ɗalibai tare da ɗaukar ma’aikata ‘yan sa ido su 130, da sauran ayyuka.

A Jihar Zamfara dai, mutum 800 ne masu cin moriyar waɗanda su ka haɗa da naƙasassu da kuma tsofaffi waɗanda za a ba kyautar N50,000 kowannen su.

Daga bisani, ministar ta ziyarci ɗaya daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira inda ta raba kayan abinci da sauran kayan masarufi, ta kuma ƙaddamar da wani laburare tare da raba kayan cin abinci ga ‘yan makaranta a ƙarƙashin Shirin Ciyar Da ‘Yan Makaranta.

Leave a Reply