SARAUNIYAR INGILA TA KWANTA DAMA

0
85

A sanarwar da Fadar Buckingham ta fitar ta ce: “Sarauniya ta rasu salin-alin a Balmoral da rana.

“Sarki da mai dakinsa za su ci gaba da kasancewa a Balmoral da wannan maraice kuma za su koma London gobe.” Dukkan ‘ya’yan Sarauniya sun tafi Balmoral, kusa da Aberdeen, bayan likitoci sun sanya ido sosai kan Sarauniya. Jikanta, Yarima William, shi ma yana can, tare da dan uwansa, Yarima Harry, yana kan hanyar zuwa Balmoral.

Firaminista Liz Truss, wacce sarauniyar ta Ingila ta nada a ranar Talata, ta ce sarauniyar ”ta samar mana da abubuwan da muke so da kuma karfafa gwuiwar mu ako da yaushe”.

Ta ce daga yanzu za a san Charles a matsayin Sarki na III.

Mulkin Elizabeth ta II a matsayin sarauniya ya biyo bayan yakin basasa, sauyi daga Sarauta zuwa Commonwealth, da karshen yakin cacar-baka da kuma shiga da kuma ficewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai.

An samu firaministoci 15 lokacin mulkinta fara wa da Winston Churchill wanda aka haifa a shekarar 1874 hada da Ms Truss, da aka haifa a 1975, shekara 101 bayan nan.

Ta kasance tana ganawa da firaminista a kowane mako tsawon mulkinta.

A fadar Buckingham da ke birnin Landan, dandazon mutane da ke jiran sanin halin da sarauniyar ke ciki sun barke da kuka bayan jin labarin mutuwar ta.

An yi kasa-kasa da tutar da ke saman fadar da misalin 18:30 na yamma.

An haifi sarauniya Elizabeth Alexandra Mary Windsor ne a Mayfair, da ke birnin Landan ranar 21 ga watan Afrilun 1926.

Leave a Reply