DAGA ABU USAIMIN
Shararran ɗanwasan gaba na ƙungiyar Manchester United mai suna Cristiano Ronaldo kusan duk lokacin da ya jefa ƙwallo a raga, yakan nufi kusurwar filin wasa ya yi tsalle sama, tare da yin ƙara “shuu” yana watsa hannaye.
Sai dai bisa mamaki a wannan karon da ya ci ƙwallonsa ta 700 a tarihin buga wasansa, wadda ya zura wa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton a filin wasanta mai suna Goodison Park, a rana 9 ga watan Oktoba, sai aka gano shi da wani sabon samfurin na nuna murnar cin ƙwallo. Ɗanwasan dai ya runtse idanunsa ne tare da langaɓar da kansa, kana ya ɗora tafun hannayensa a kan ƙirjinsa.
Kodayake wannan sabon salo da ya fito ba a ba shi suna ba, amma ya maye gurbin wanda ya saba yi a bayaan
Tuni abokan karawarsa da ke Manchester United ɗin wato Antony Santos da kuma Alejandaro Gernacho suka bi sahun ɗanƙasar Portugal ɗin wanda ya zame musu madubin dubawa.
‘Yanwasa da dama sun bi sahun takwarorin nasu na Manchester wurin koyi da Ronaldo. Ɗanwasan ƙungiyar Man City wanda yake bugawa a ɓangaren matasa ‘yan ƙasa da shekara 21 wato Carlos Borges shi ma ya yi wannan salo lokacin da ya zura ƙwallo ta uku a karawarsu da Manchester United.
Harwayau ɗanwasan ƙasa Nigeria wato Ademola Lookman da kuma takwaransa Demiral su ma dai ba a bar su a baya ba. ‘Yanwasan na Atlanta sun yi wannan salo ƙwallayen da suka fara zurawa a wasan da suka yi da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli.