SHIN TAYAYA KIRARIN ‘KANO NA ”KANO JALLABAR HAUSA YA GURƁACE??

0
205

 

Mun yi hira da Kachallan Kano maigirma Malam Magaji Galadima ta waya dazu, kuma ya ƙara min haske a kan asalin kirarin da dalilin da ya sa ya gurbace .

Kachalla ya ce min kirarin ya samu gurbacewa ne a dalilin kuskuren ɗab’i da aka yi a labarin “An Ki Cin Biri An Ci Dila” da ke cikin littafin “Magana Jari Ce” na Abubakar Imam. Wannan kuskure na dab’i an yi shi a wannan babi a cikin zantawar Dan’iya da Daudu, wasu shaƙiyyan birni dake sane da yankan aljihu a kasuwar Kurmi, anan ne aka rubuta kirarin ba daidai ba, maimakon a rubuta Jallabar Hausa, sai aka rubuta Jalla babbar Hausa.

A cewar Kachallan Kano, tahirihin wadannan mutanen Jallaba da na kawo haka yake. Sai dai ba kamanceceniyar Jallabar Sudan da Kano ta fannin cinikin bayi da kasuwanci da yaki ne ya sa ake yi wa Kano kirari da “Kano Jallabar Hausa” ba.

Ya ce akwai riga da su ire iren waɗannan Larabawa ke sakawa wadda ita ma a ke kiranta da “Jallaba”. Baƙaken Larabawa dake zaune a Kano kamar Usman Jallaba, ainihi Usman mai Jallaba ake kiransa daga baya ake taƙaitawa ya koma Usman Jallaba. Akwai sauran irinsu Sarkin Fada Zimit da Musa Gashash da su Matawalle Malam Munir duk ita suke sakawa. Ita wannan riga kamar cikar ado ce, domin sai an cancada ado sannan kuma a dora ta a sama kamar alkyabba. Jallaba na kama da alkyabba, ita ma gabanta a bude ya ke. Jallaba na da igiyar ƙullewa guda uku, da wajen zura hannaye kuma ba ta da kokuwa (hood).

A cewar Kachalla, kalmar Hausa da aka yi amfani da ita a wannan kirari ana nufin Sakkwato ko kuma daular Usmaniyya. Bisa ga kasaitar Kano a matsayin garin da ya fi girma da shuhura da arziki a kasar Hausa, shi ya sa ake yi mata kirari da “Jallabar Hausa”, wato cikar kwalliyar kasar Hausa.

Kachallan na Kano har ila yau yace Jalla babbar Hausa bai bada wata ma’ana ingattacciya ba in aka sheƙe aka tankaɗe kalmomin. Ya ƙara da cewa hatta maigirma marigayi Ɗanmasanin Kano a jawabansa Jallabar Hausa ya ke cewa ba Jalla babbar Hausa ba.

#ranarhausa2022“`

Leave a Reply