SHUGABAN ƘARAMAR HUKUMAR KARU DA KE JIHAR NASARAWA YA SANYA DOKAR HANA FITA AKAN MATSALAR RASHIN TSARO DA KE ADDABAR YANKIN

0
162

 

 

Mista James Thomas, shugaban zartarwa na karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa, ya sanya dokar hana fita a yankin karamar hukumar a matsayin wani mataki na dakile barazanar tsaro.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Mista Danbaba Magaji, babban mataimaki na musamman (SSA) ga shugaban kan harkokin yaɗa labarai.

A cewar sanarwar, shugaban majalisar ya ɗauki matakin ne bayan wani taron faɗaɗa zaman lafiya da tsaro da yayi da dukkanin jami’an tsaro na majalisar a ranar Litinin.

Ya ce ana sa ran dokar taɓacin za ta fara aiki ne a ranar Alhamis 11 ga watan Agusta, 2022, daga karfe 10 na dare zuwa karfe 6 na safe har zuwa wani lokaci.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Ya zama wajibi a gare mu mu dauki kwararan matakai don dakile matsalar tsaro a yankinmu, duk da cewa muna samun zaman lafiya a karamar hukumar Karu.

“Amma dole ne mu yi aiki ba tare da gajiyawa ba da kuma ɗaukar duk matakan tsaro don tabbatar da cewa muna zaune lafiya, la’akari da kusancinmu da Abuja da masu aikata laifuka suna amfani da hakan a matsayin zabin cin gajiyar hakan.

“Saboda haka, za mu ɗauki wannan matakin a matsayin matakan kariya daga ranar Alhamis, 11 ga Agusta, 2022, har zuwa wata sanarwa don aiwatar da dokar hana fita daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.”

Ya ce dokar ta hana zirga-zirga da zarar ta fara aiki, za ta takaita zirga-zirgar ababen hawa, da rufe dukkan gidajen sinima, mashaya da gidajen abinci da sauran ayyukan da ke ƙaramar hukumar Karu.

Leave a Reply