Shuguban hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA) Gianni Infantino ya nemi ƙasar Russia da Ukraine da su tsagaita wuta har tsawon wata guda, don a samu damar gabatar gasar cin kofin duniya cikin salama.
Gasar dai za a fara ta ne a ranar Lahadi mai zuwa 20 ga watan nan da muke ciki.
Infantino ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa shugabannin ƙasashe bayani a taron G20.
Ya ƙara da cewa gasar cin kofin duniya, wani taro ne yake ba da gamammiyar dama ga kowa, don samun haɗin kai da zaman lafiya.
Fiye da mutane biliyan 5 ne za su kalli wasan a duniya baki ɗaya.
“Don haka abin da zan jawo hankalinku shi ne, ku dakata na tsawon wata guda har sai an kammala gasar.” Ya faɗa a taron da aka gabatar a tsibirin Bali da ke ƙasar Indonesia.
Ya kuma yi ishira zuwa ga wasu shawarwari da ka iya zama mafita “ko bin duk wani abu da ka iya jawo zaman teburin sulhu.” a matakin farko na samun zaman lafiya.
“Ku ne shugabannin duniya, ku ne kuke da damar samar da tarihi mai kyau.”
Harwayau shuguban kwamitin wasanni na duniya wato (IOC) Thomas Bach ya roƙi gwamnatoci da su yi la’akari da hazaƙar ‘yanwasanni bisa gasannin da suka gabata, ba wai a zaɓe su saboda wani ra’ayi na siyasa ba.
“Wasannin duniya za su faɗi ƙasa wanwar matuƙar za a shigar da siyasa cikinsu. Ya kamata a turo wakilai waɗanda za su yi ɗa’a, musamman idan ya zamana ƙasashen na ƙalubalantar juna” Bach ya faɗi hakan ne a taron da ya gudana a Bali.
Ƙungiyoyin hukumomin wasanni daban-daban sun amince da tsame ƙasa Rasha daga harkokin wasanni, biyo bayan mamayewar da take yi wa ƙasar Yukiren.