Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda tare da ƙwato makamai a Binuwai da Katsina

0
211
Dakarun 'Operation Hadarin Daji' a bakin aiki
Dakarun 'Operation Hadarin Daji' a bakin aiki

Dakarun ‘Operation Whirl Stroke’ sun fatattaki ‘yan ta’adda a yayin wani artabu da ya gudana a ranar 15 ga Yuli, 2022 a wani samame da su ka kai a yankin Chito da ke gundumar Sankera a Ƙaramar Hukumar Ukum ta Jihar Binuwai.

Sojojin sun ci karo da wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne waɗanda su ka buɗe wa dakarun wuta da harbin kan mai uwa da wabi.

Dakarun sun maida martani da ƙarfin wuta mai nauyi, su ka yi nasarar kashe ‘yan bindiga guda uku yayin da wasu su ka tsere.

Sojojin sun binciko maɓoyar ‘yan ta’addar tare da gano babura 18 da su ke amfani da su wajen addabar yankin.

A wani labarin makamancin wannan, dakarun ‘Operation Hadarin Daji’ sun kai samame a ƙauyen Palale Jaja da ke Yankin Ƙaramar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina inda su ka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu tare da ƙwato kayayyakin da su ka haɗa da bindigogi biyu samfurin AK-47 da tsakiyar albarusai da babura shida da wayoyi biyu da kuma fakitin magunguna masu sa maye.

Rundunar sojoji ta ta yaba wa dakarun ‘Operation Whirl Stroke’ da na ‘Operation Hadarin Daji’ bisa namijin ƙoƙarin da su ka yi.

Haka kuma ta yaba wa jama’a da ke bai wa sojoji bayanai game da masu aikata laifuffuka a yankunan su.

Leave a Reply