Daga Halima K/Mashi
Wane tanadi ku ka yi wa jikin ku a lokacins anyi dan gyara jikin ku da fatar ku, kasan cewar lokacin sanyi jiki yakan bushe ga hari da sanyi kan kai wa lafiya a wasu lokutan.
Ana samun Waɗan nan matsalolin a lokacin saiyi kamar haka..
Bushewa da tsagewar leɓe.
Tsagewar ƙafa.
Fatar jiki tana ƙaiƙayii ko ma ta tsage.
Ko fuska ta yi kaushi. (Waskane)
Bushewar fatar kai.
Ƙaiƙayin kai da zubewar gashi. Har gaban mace yakan bushe yana ƙaiƙayi ko ma ya tsage. Bushewar Tafin hannu ko kaushi a tafin hannu.

Waɗannan abubuwan sukan faru a lokacin sanyi.
Binciken masana ya nuna cewa cin kayan marmari irin su gwada, abarba ayaba, kankana da sauran su. Su na taimakawa inganta lafiyar jiki a lokacin sanyi, haka yin amfani da abinci ko abin sha mai ɗumi kamar shayi ko kunu, suna taimakawa jiki da maƙoshi gurin rage bushewa a lokacin sanyi.
Haka shan ruwa mai yawa yana ƙarawa jiki lafiya a lokacin sanyi, ‘ya’yan itace rinsu mangwaro timatir da duk masu bitamin C suna taimakawa gurin hana fashewar wasu sassa na jiki irinsu fason ƙafa.
Game da fatar jiki kuwa shafa mai me maiƙo yana taikawa fata daga bushewa, zaku iya amfani da man kaɗaya man kwakwa man zaitun man alayyadi, waɗan nan mayuka suna taimakawa fata ta yi laushi.

yawan amfani da tufafi ma su kauri saka safar ƙafa domin rufe ƙafafu, suna taimakawa jiki ya rage bushewa. Shafa man zaitun da zuma a hannu yana taimakawa gurin sa hannu ya yi laushi.
Yin tsarki da ruwan ɗumi akai akai da kaucewa yin matsi da wasu abubuwa na kayan mata yana taimakawa gaban mace rashin bushewa ko tsagewa haka nan yana hana cutuka irin su sanyi mara su samu gindin zama a gaban mace.

Yin amfani da kayan ƙamshi cikin naman kazar Hausa musamman tafarnuwa a dafata da kayan ƙamshi ayi ta da romo a sha romon yana taimakawa matantakar mace a lokacin sanyi tare da hana yamushewar fatar jiki shan madara ko ɗanyan kwai da kayan marmari da safe kafin cin wani abu mai nauyi yana taimakawa gurin hana ƙafewar ni’imar mace a lokacin sanyi.
Bushewar gashin kai da kaɗewar gashi suna faruwa sosai a lokacin sanyi. Yana da kyau muna rufe gashin kanmu,tare da shafa mai na gashi sau biyu a rana,wanke kai da ruwan dumi da kanwa ko karkashi a shafa man kwakwa ko ɗanyan man shanu a haɗa da man alayyadi yana hana zubewar gashi a lokacin sanyi.