Labarai

KAMFANIN A A RANO YA ƘARYATA BATUN RAGE FARASHIN LITAR MAN FETUR ZUWA 400

A jiya ne bayanai suna rinƙa zagayawa a kafafen sada zumunta cewa kamfanin A.A Rano Nigeria ltd ya rage farashin litar man fetur a gudajen mansa daga N550 zuwa N400 biyo bayan ɓullar rahoton karyewar farashin ɓan a depot-depot na Nigeria.

Sai dai a wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ta nuna bayanan a matsayin shifcin gizo.

“Shugabannin kamfanin AA Rano Nigeria Ltd su na masu karyata wani bayani na karya kuma mai ɓatarwa dangane da saida fetur a N400 a wasu zababbun gidajen mai, Ayi watsi da wannan labari na karya kaco-kam.” Imji sanarwar.

Kamfanin A.A Rano ya ce maganar saida litar fetur a N400 sam ba gaskiya ba ne, bai karya farashinsa ba.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button