Tinubu bai bunƙasa Legas lokacin da ya yi gwamna ba, dillancin tara haraji da kashe dimokiraɗiyya kawai ya yi – Bwala, kakakin kamfen na Atiku 2023

0
797
Bola Ahmed Tinubu

DAGA ALI KANO

Yayin da zaɓen 2023 ke ƙara gabatowa, kakakin yaɗa labaran manyan jam’iyyu biyu, wato PDP da APC, na ci gaba da antaya wa ɓangarorin junan su zafafan raddi.

Ciki makon jiya, Kakakin Yaɗa Kamfen ɗin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Daniel Bwala, ya yaɓa wa Bola Tinubu da ke takarar shugaban ƙasa a APC zafafan raddi.

Bwala ya yi iƙirarin cewa masu tutiya da Tinubu ya bunƙasa Legas lokacin da ya na gwamna, to ba gaskiya ba ne. Bwala ya ce babu abin da Tinubu ya yi sai karɓar haraji kawai, amma ba shi ya gina wuraren da ya riƙa karɓar harajin ba.

Ya ce: “Idan za a yi duba da idon basira, za a ga cewa Tinubu ba Legas ya gina ba, haraji ya riƙa karɓa daga manyan kamfanoni, masana’antu da hukumomin gwamnatin tarayya kawai.

“Lokacin da ya yi gwamna daga 1999 zuwa 2007, bai gina wani abin kirki ba. Haraji ya riƙa karɓa. Ya tarar akwai tashoshin jiragen ruwa, tashar jirgin sama, sannan hedikwatar bankunan Najeriya duk a Legas su ke. Kuma can ne cibiyar kasuwanci. Don ya riƙa karɓar haraji da yawa ai ba abin mamaki ba ne.

“Kuma a lokacin an yi zargin cewa kamfanin da gwamnatin Legas ta bai wa kwangilar karɓar harajin, na Tinubu ne.

“Ashe kenan duk wanda aka ce masa ga aikin karɓar haraji, idan ka karɓa, ka ɗauki kashi 30%, ai dole ya yi ƙoƙari.”

Da ya koma batun dimokraɗiyya kuwa, Bwala ya ce lokacin da Tinubu ya na gwamna babu wanda ya kai shi yunƙurin kashe dimokraɗiyya a ƙasar nan.

Ya ce: “Ba a taɓa yin gwamnan da ya yi amfani da ‘yan majalisar jihar sa ya tsige mataimakan sa mabiyi da mabiyi har uku ba, sai Bola Tinubu.

“Sannan kuma duk mutanen da ya ke ɗorawa a siyasa, ba farin jinin jama’a ko karɓuwar su ce ke kai su ga nasara ba, sai ƙarfa-ƙarfar Tinubu, inji Bwala cikin wasu gajerun bidiyon da riƙa yaɗawa a shafukan sada zumuntar sa na soshiyal midiya.”

Daga nan kuma Bwala ya koma batun manufofin APC a ƙarƙashin mulkin Tinubu idan ya ci zaɓe, ya ce ba wani sabon tunani ba ne aka bijiro da shi, “daftari ne da manufofin da marigayi Abiola ya yi kamfen da su aka wanko.”

Baya ga wannan wankiyar daftarin manufofin Abiola, Bwala ya ce taken manufofin wanda a Turance ake kira “Renewed Hope”, ya nuna kenan duk masifar da aka shiga a gwamnatin APC za a sake maimaitawa kenan.

“Idan kuma sun ce wata sabuwa ce, to dai waɗanda su ka zauna su ka tsara manufofin APC a 2015, Tinubu ne ya haɗa wa Buhari su. Idan yanzu sun sake kawo wani salo daban, tunda su na cikin wannan gwamnatin, ai hakan ya na nufin kenan salon yanzu da wannan gwamnati ke kai, ya kai Najeriya ya baro kenan.

“Kuma irin kamfen ɗin da su ke yi, su na nuna gwamnatin Buhari ta gaza,” cewar Bwala.

Da ya ke magana kan Daraktan Yaɗa Labaran Kamfen ɗin TInubu, wato Festus Keyamo, Bwala ya ce ai su Keyamo ɗin ne su ka maka Tinubu kotu lokacin da ya na gwamna, su ka ce ya yi ƙaryar makarantun da ya yi iƙirarin cewa ya yi karatu.

“To abin da za a ƙara lura a nan, Keyamo ɗin nan da ke ta ɓaɓatun tallar Tinubu a yanzu, shi ne dai a wancan lokacin ya ci gaba da maka Tinubu kotu, har zuwa Kotun Ƙoli, ya na ƙalubalantar takardun makarantar sa.

“An kori ƙarar a Kotun Ƙoli saboda Keyamo bai haɗa kwafe-kwafen takardun hujjojin sa da rantsuwar kotu (affidavit) ba, amma kotu ba cewa ta yi Tinubu na da gaskiya ba,” inji Bwala.

Ya nanata cewa saboda tun farko Keyamo bai je kotu ya yi rantsuwa ba, ya haɗa kwafen takardar rantsuwar sa kwafen hujjojin dalilin maka Tinubu kotu, shi ya sa aka kori ƙarar kawai.

Leave a Reply