UBA DA ƊANSA SUN RASA RANSU A WATA RIJIYA A WUDIlI

0
165

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani Dattijo mai suna Malam Bala mai shekara 60 da ɗansa Sunusi Bala ɗan shekaru 35 waɗan da suka nutse a wata rijiya.

Mutane biyun sun rasa rayukansu ne a Sabon Garin Bauchi cikin ƙaramar hukumar Wudil a yayin da su ke kwashe ruwa daga rijiya.
Mai magana da yawun hukumar Saminu Abdullahi ya bayyana yadda lamarin ya faru da safiya
Talata.

A cikin wata sanarwa da ya fitar Saminu Abdullahi ya ce an kirawo ofishin kashe gobara na Wudil da misalin ƙarfe 11: 30 na safe ta wayar wani Isma’il Idris.

Ya sanar da mutuwar Uba da Ɗan waɗanda a ka kira su domin su kwashe rijiya sun yi nasarar kwashe rijiyar amma sai ɗan ya koma domin share rijiyar amma sai ɗan ya maƙale. Mahaifin ya koma domin ceto ɗan na sa amma sai suka maƙale gaba ɗaya sakamako rashin iska an fito da su a sume ka fin daga baya suka rasa ransu.

Leave a Reply