Ummita ta kira ni sati guda da ya wuce ta ce tana da tambaya : Inji Malam Aminu Daurawa

0
94

.

Babban Malamin nan Malam Aminu Daurawa da ke jihar Kano ya ce, Ummita ta kira ni sati guda da ya wuce ta ce tana da tambaya, tana son zata auri wani ɗan Ƙasar Chaina amma iyayanta sun ƙi yarda.

Ya faɗi haka ne a wani faifan Vidiyo da ya wallafa a shafinsa.
Malamin ya ce ya bata shawara guda biyar domin iyayenta sun yi gaskiya da suka ƙii yarda duk da cewa ta ce ɗan Chanan ya musulunta.

Ya bata sharawa ta nemi Imagiresho don tabbatar da cewa ya shigo ƙasar da izini.

A san sana”arsa

Ta nemi Sarkin yan Chaina su yi bincike a san asalinsa.

A nemi Ofishin jakadancinsu

Sannan a haɗa su da Hisba su koya masa addini.
Yace sunyi tattaunawa ta kusan minti goma shabiyar, amma katsam sai ya samu labarin cewa wani ɗan Ƙasar Chaina ya kashe budurwarsa, Ya yi addu a Allah ya jiƙan Ummita kuma ya  yi kira ga mahukunta lallai su hukunta makashin daidai da laifinsa.

Leave a Reply