WASU ‘YAN FASHI DA MAKAMI SUN MAMAYE GIDAN JARUMI TARE DA NEMAN KUƊIN FANSA

0
162

 

A daren ranar Litinin 8 ga watan Agusta ne wasu ‘yan fashi da makami suka mamaye gidan fitaccen jarumin wasan barkwanci na Nollywood, Afeez Oyetoro aka Saka, jihar Ogun.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan fashin sun bƙaci a biya su kuɗi Naira miliyan 20, kuma a lokacin da suka kasa samun kudin ne suka yiwa jarumin dukan tsiya inda suka kwashe wayoyinsa da kwamfutar tafi-da-gidanka da sauran kayan da za su iya dauka.

Abokin jarumin, Kayode Soaga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata.

“Mutanen sun shiga gidansa da misalin karfe 2 na safe, ɗauke da manyan bindigogin Pump action bindigogi, kuma suka kori masu gadin sa.

“Wasu gidaje uku da ke kan titi an yi musu fashi da barna. Sun karya shedar sata, kai tsaye suka je wurinsa suna neman Naira miliyan 20 ko ransa, suna barazanar kashe shi. Sai dai ya roƙe su, sun koma miliyan uku amma jarumin ya ce ba shi da shi.

“Sun azabtar da shi tare da kwashe dukkan wayoyin Android, kwamfutar tafi-da-gidanka na iPhones da duk tsabar kudi da ke cikin gida da katin ATM. Waɗannan mutanen sun zo ne da POS don kwashe kudi a asusunsa.

Leave a Reply