YADDA ABINCI KE SARRAFUWA A JIKIN ƊAN ADAM.

0
171

 

Yau za mu yi bayani ne akan yadda abinci yake sarrafuwa ko muce narkewa kana yayi amfani a jikin ɗan Adam wajen samar da kuzari a wajen ayyukanmu na yau da kullum.

Amma kafin mu fara, ya kamata mu san nau’in abinci fa guda biyar ne, wannan zai taimaka mana wajen ganewa

1. Carbohydrates: A Hausance ana kiran wannan nau’in abinci da “abinci mai ƙara kuzari ko kuwa bada ƙarfi ga ɗan Adam” yawancin abincin da muke ci yau da kullum irin wannan abinci ne, wato carbohydrates. Misalinsu sun hada da Shinkafa, Masara, Doya, Dankali, Fulawa da makamantansu.

2. Proteins: Za mu iya kiran wannan kalar abinci da suna “abinci mai gina jiki.” Wannan kalar abinci ya fi amfani ne ga yara da marasa lafiya, musamman wanɗanda suka ji ciwo.
Karancin wannan kalar abincin shi ke jawo ciwon nan da ake kira kwarshookor wanda ƙananan yara ke kamuwa dashi. Sai ka ga yaro ya rame ya kwanjame. Misalan abinci masu gina jiki sun haɗa da: kifi, nama, wake, da makamantansu.

3. Fats and oil: (Abinci masu maiko).
Kamar yadda sunan ya bayyana, waɗannan nau’in abincin su ma suna bada ƙarfi musamman a lokacin da carbohydrates suka yi karanci a jikin mutum. Wannan kalar abinci suna da matukar amfani ga jikin Ɗan Adam da kuma dabbobi. :Misalansu sun haɗa da: gyaɗa, manja, man gyaɗa da dai sauransu.

4. Vitamins:
Waɗannan wasu sinadaran abinci ne dake taimakawa wajen gyara jiki da makamancin haka. Ana samun sinadaran vitamins ne a jikin ‘ya’yan itatuwa da kayan lambu. Karancin vitamins a jikin Ɗan Adam yana jawo
matsaloli da dama.
misali ƙarancin vitamin yana jawo rashin gani musamman ga manyan mutane.

5. Minerals:
Amfanin minerals kusan ɗaya ne da vitamins, wato kamar gyaran jiki, ƙara lafiya da makamantansu.
Ana samun minerals ne a ganyaye, ’ya’yan itatuwa da sauran kayan lambu kamar mangwaro, tuffah, albasa, lemun zaki dana tsami da dai sauransu.

To yaya yake kasancewa idan mutum ya ci abinci, sai ya narke kuma ya samar da waɗannan kala-kalar sinadarai da abinci da jiki ke buka ta?

 

A duk lokacin da mutum yasa abinci a bakinsa ya tattauna, abincin zai haɗu da yawu wanda yake ɗauke da sinadarin ptylin. Shi dai yawu, yana fitowa ne daga wasu wuri da ake kira salivary glands waɗanda suke rufin baki, wato saman baki, da kuma ƙasan harshe. Sinadarin ptylin yana chanja starch (wani nau’in na carbohydrate) zuwa maltose. Daga nan abincin zai wuce ta makogoro, wucewa da ake kira “peristaltic movement”. A makokoron mutum da na dabbobi akwai wasu hanyoyi guda biyu: hanya ta farko tana ɗaukan iska ne, ta biyun kuwa tana daukan abinci ne.

A lokacin da abinci ya shiga makogoro, wani ɗan nama da ake kira “flap” zai toshe hanyar iska, wanda a duk lokacin da aka samu matsala shi flap din bai toshe hanyar iskan ba, to abinci zai shiga hanyar iskan wanda yake jawo shakewa. Bayan abincin ya wuce ta makogoro, zai wuce zuwa can ciki inda za’a ajiyeshi na awa biyu zuwa hudu, ana kuma sake shi daga lokaci zuwa lokaci ta hanyar budewa da kullewan ‘pyloric sphincter.’

Daga nan abincin zai dawo ruwa-ruwa wanda ake kira da “chyme” wanda za’a kwabashi da sinadarin gastric juice wanda yake dauke da sinadarai irinsu hydrochloric acid, pepsin da rennin. Shi dai pepsin yana amfani ne wajen canja abinci mai gina jiki wato proteins zuwa wasu yan units wanda ake kira peptones. Wannan abincin zai bar pyloric sphincter ya shiga “duodenum” bile duct don ya dauko madaci daga gall bladder zuwa duodenum. Shi dai madaci (wanda a Turance ake kira bile) yana dauke ne da waɗansu sinadarai da gishiri (salts) irin su sodium hydrogentrioxocarbonate (NaHC03), bilirubin da biliverdin.

Abincin da yake duodenum yana ɗauke da pancreatic juice wanda ya fito daga pancreas ya bi ta pancreatic duct. Shi dai pancreatic juice yana dauke ne da sinadaran lipase da amylase da kuma zymogen wanda wani lokaci ake kira da trypsinogen. Shi sinadarin lipase yana amfani ne wajen narka kitse da mai ya kuma canja su zuwa fatty acid da kuma glycerol. Shikuma amylase yana canja starch ne zuwa maltose. Shikuma trypsinogen, at normal conditions baya aiki, yana aiki ne kaɗai a lokacin da wani sinadari wanda ake kira da enterokinase ya taɓa shi.

Daga nan abincin wanda ya dawo ruwa-ruwa zai shiga ileum ta hanyar “peristaltic movement”. Shi kuwa bangon ileum yana fidda wani ruwa wanda yake dauke da sinadarin erepsin, maltase, sucrase, lactase da lipase. Sucrose yana narka suga (sucrose) zuwa fructose, shi kuma lactase yana canja lactose (milk sugar) zuwa glucose da kuma galactose bayan abinci ya gama narkewa, wanda jikin bata bukatarsa a wannan lokacin ana ajiye shi, wato storing, a yanayi da ake kira glycogen a karkashin fatan mutum da kuma wadansu wurare.

 

Bayan haka abincin yakan narke a cikin jini ya tafi zuciya wanda take pumping dinsa zuwa jijiyan arteries at high pressure. Arteries, wasu jijiyoyi ne masu kaurin gaske. Allah ya halicce su da kauri ne saboda jinin da yake fita daga zuciya yana fita ne da karfin gaske. Arteries suna rabuwa zuwa kananan jijiyoyi na arterioles, suma arterioles suna rabuwa zuwa kananan jijiyoyi wanda ake kira capillaries. Capillaries suna haduwa suyi forming jijiyoyi ‘yan babba wanda ake kiransu da venules. Venules suna haduwa su bada babban jijiya wato veins wanda take maida jinin zuwa zuciya. Jijiyoyin veins basu da kauri sosai Kamar jijiyoyin arteries sabida jinin da yake komawa zuciya bashi da karfi kamar jinin da yake fita daga zuciya.

Atakaice wannan shine yadda abinci ke sarrafuwa cikin jikin Ɗan Adam ya narke ya zama sinadarai daban-daban don yin amfani ga cikin Ɗan Adam.
Allah shi ne mafi sani.

Leave a Reply