Yadda kyautar motocin ɗaukar Gawa ya sanya al’ummar Garin Bichi cikin Farin ciki marar misaltuwa

0
208
Motocin ɗaukar gawa.

 

DAGA RUMAISA ALIYU

Sau tari masu hannu da shuni sukan faɗsaɗa kyaututtukan su ne ga rayayyu don su gani su yaba , amma akan manta akwai ‘yan’uwansu da dama da ke kwance a maqabartu waxanda su ma suke bauqatar taimakonsu. Wannan taimako ya zama wajibi ga kowa don ko ba komai mutuwa tana kan kowa sannan maqabarta nan ne dai gida na qarshe da kowa zai je ya kwanta.
A ranar juma’a 4 ga watan Nuwamba , 2022 ne , Alhaji Jamilu Kabiru Bichi (Sabon Shafi) ya saya wa garin Bichi motocin xaukar gawa guda (3) tare da bayar da kyautar baburan hawa ga masu hidimtawa maqabartun yankin.

Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da Alhaji Jamilu Kabiru Bichi (Sabon Shafi)

Garin Bichi yana fama da matsalar motar xaukar gawa. Duk lokacin da aka samu rashi ana fuskantar matsala ko dai a yi ta kame-kame ko kuma wani ya bayar da tashi motar ta hawa a kai mamacin.
Daga cikin amfanin da motar take yi, wanda rashinta ya shafi al’umma , tana taimakawa har wasu daga cikin qauyukan garin na gabas da yamma wajen xaukar mamaci daga asibiti zuwa ga iyalinsa in an samu rashi domin a suturta shi kamar yacce addini ya umarta.
Alhaji Jamilu Kabiru Bichi (Sabon Shafi) ya bayyana babban maqasudin abim da ya ja hankalinsa har ya yi wannan hangen savanin tunanin yawancin a l’umma, inda ya nuna babban abin da ya tayar masa da hankali shi ne wata rana ya ci karo da iyalin wani mamaci rungume da gawarsa a cikin mashin mai kafa uku (Adaidaita sahu) wanda har ana hango qafafun mamacin sun zuro waje. Ganin hakan ya sa shi zubar da kwalla wanda daga nan ya kudurci aniyar samar da motoci don xaukar gawa. Kuma Allah ya dafa masa burinsa ya cika, ya samar da motocin gami da Babura don taimakawa masu kula da maqabartum.
A ranar cikin amincewar Allah, Mai

Martaba Sarkin Bichi, Alh. Nasiru Ado Bayero ya qaddamar da bayar da waxannan motovin ga dagatan yankunan da za’a ba wa motocin, tare da daxa mika mukallan sababbin babura kirar (Classic) ga wasu daga cikin fitattun mutane da suka yi suna wajen hidimtawa maqabartun ciki da wajen garin Bichi.

A jawabin Hakimin Bichi, Alh. Abdulhamid Bayero yayin gabatar da Alh. Jamilu (Sabon Shafi) a gaban sarkin na Bichi , ya yaba masa a bisa wannan qoqari da ya yi tare da yi masa addu’ar fatan alkhairi. Taron ya samu halartar hakimai da ‘yan majalissar sarki da dagatai da limamanan masarautar da sauran al’ummar gari. Daganan Tafidan Bichi ya zarce makabarta ziyara, inda ya soma da qabarin Mahaifinsa Marigayi Alh. Kabiru Bichi ya yi masa addu’a tare da dukkanin abokanin kwanciyarsa. Sannan kuma duba yanayin magudanan ruwa da ke maqabartar tare da ganin wasu ayyukan da maqabartar take buqata da zai yi nan ba jimawa ba Insha Allah. An yi taro lafiya an kammala lafiya.

Leave a Reply