Yadda taron tunawa da Mahmoon Baba-Ahmed da ƙungiyar Alƙalam ta shirya ya gudana

0
101

Wani sashe na mahalarta taron
Wani sashe na mahalarta taron

ƘUNGIYAR marubuta ta Alƙalam da ke Kaduna ta gudanar da taron tunawa da fitaccen ɗan jarida kuma marubuci, marigayi Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed, tare da ƙaddamar da littafin sa na ƙarshe a duniya.

Taron, wanda ya gudana a yau Alhamis, 9 ga Fabrairu, 2023, a Gidan Arewa, Kaduna, ya zo a daidai ranar da Mahmoon ya cika shekara biyar cif da rasuwa.

An buɗe taron da misalin ƙarfe 11:44 na rana da addu’a, wadda Alhaji Balarabe Idris Jigo ya yi. Daga nan sai shugaban tashar talbijin da rediyo ta Liberty da ke Kano, Alhaji Muhammad Iskil Abdullahi, wanda shi ne ya wakilci shugaban taron, wato Ciyaman na Liberty, Dakta Ahmed Tijjani Ramalan, ya gabatar da jawabin buɗe taro.

A cikin jawabin nasa, ya ambato irin kusancin sa da tarayyar sa da marigayin. Ya ce, “Tabbaci haƙiƙa, Mahmoon Baba-Ahmed ya rayu ne wajen gwagarmayar kawo sauyi ga ci-gaban Arewa da Nijeriya baki ɗaya, wanda sanin da na yi wa Mahmood Baba-Ahmed a kafafen yaɗa labarai, Allah cikin ikon sa a shekarar 1992, tsohon gwamnan Jihar Kaduna na wancan zamani, Alhaji Dabo Lere, ya naɗa ni kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kaduna, a wancan lokaci ana kiran mu ‘advisers’, shi kuma Mahmoon shi ne darakta a wannan ma’aikata.”

Daga hagu: Muhammad Iskil, Hakimin Gundumar Kawo Alhaji Jibrin Magaji Hassan, da Hakima Abdullahi K/Mashi
Daga hagu: Muhammad Iskil, Hakimin Gundumar Kawo Alhaji Jibrin Magaji Hassan, da Hakima Abdullahi K/Mashi

Ya ci gaba da cewa, “A gaskiya mun yi zaman amana da shi Malam Mahmoon. Kuma shi mutum ne mai aiki tuƙuru, ba kuma don ya samu wani abu ba ko yabo, ya na yi ne fisabilillahi a matsayin sa na ɗan jarida.

“Na tuna, mu na aiki tare da shi rikicin Zangon Kataf ya ɓarke. Malam Mahmoon ya nuna ƙwarewa matuƙa wurin amfani da kafafen yaɗa labarai na Jihar Kaduna wajen dakushe wutar rikicin da kuma kwantar da hankalin jama’ar Jihar Kaduna.

“Haka kuma Mahmoon shi ne ya ƙirƙiro da wata jarida mallakin Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna mai suna ‘The Dawn’, kuma shi ne ya kasance babban editan ta. A wancan zamani kowane mako ake wallafa ta. Babu shakka jaridar ‘The Dawn’ ta ba da gudunmawa matuƙa wajen tallata gwamnatin Jihar Kaduna a wancan lokaci.

“Cikin ikon Allah, Allah ya ba ni damar buɗe gidan Rediyon Liberty a Kaduna, nan da nan Liberty ta samu ɗaukaka. Amma sai mu ka lura mu na da buƙatar inganta ɓangaren Hausa a tashar namu, musamman ɓangaren labarai da al’amuran yau da kullum. Sai mu ka ga babu wanda ya kamata ya shigo ya ba mu gudunmawa sai marigayi Malam Mahmoon. Daga shigowar sa ne ya ƙirƙiro da shirye-shirye tari masu ma’ana da kuma ban-sha’awa.

“Ba za mu manta da ‘Dimokuraɗiyya’ ba da kuma ‘Tambihi’, inda ake gayyato ‘yan siyasa da manyan masu faɗa a ji, da kuma ‘Magamar ‘Yanci’, da sauran su. A yau batun da ake yi, Liberty ta zama jagora a ɓangaren labarai da sauran shirye-shirye.”

Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan ya ƙara da cewa, “Babu shakka, tarihin nasarorin Liberty ba zai taɓa cika ba ba tare da gudunmawar da Mahmoon Baba-Ahmed ya bayar ba.

“Babban ƙalubalen da mu ke ciki shi ne: Malam Mahmoon tasa ta yi kyau, Allah ya gafarta masa, shin akwai sauran ‘yan jarida irin su Mahmoon Baba-Ahmed kuwa, wanda za su yi aiki tuƙuru ba don ‘brown envelop’ ba, ba don wani biyan buƙatar kan su ba? Wannan shi ne tambayar da na ke so a wannan wuri a ba da amsa.”

Shugabar ƙungiyar Alƙalam, Hajiya Halima Abdullahi K/Mashi, ta gabatar da jawabin maraba ga mahalarta taron, sannan kuma ta ba da taƙaitaccen tarihin ƙungiyar Alƙalam. Ta ce, “Ita dai wannan ƙungiya, ƙungiya ce ta marubuta littattafai ne da ke zaune a Jihar Kaduna, su ka haɗu, su ka kafa ta a cikin shekarar 2012. Bayan kwana ɗaya da ƙirƙirar ƙungiyar, sai mu ka tattara mu ka je mu ka sami Baba Mahmoon a ofishin sa, mu ka yi masa bayani a kan cewa ga yunƙurin mu na kafa ƙungiya, don mu tattara kan mu wuri ɗaya. Ya karɓe mu hannu biyu-biyu, ya kuma ce mana daga yau wannan ofishin nawa, shi ne ofishin ƙungiyar ku, domin ƙungiya ba ta zama ba ofishi.

“Sannan kuma da taimakon shi mu ka haɗu, mu ka raɗa mata suna Alƙalam. Haka kuma da taimakon sa mu ka haɗa mata kuɗin aski, wato rijista kenan. Baba Mahmoon ya karɓe mu hannu biyu-biyu, kuma ya yi mana dukkan iyakacin ƙoƙarin sa don ya ga cewa ƙungiyar ta ɗore a lokacin, a ƙarƙashin shugabancin Baida’u Muhammad Gada.

“A ci gaba da yi mana jagoranci, mun shirya manyan taruka guda biyu, na farko ƙaddamar da ƙungiyar da mu ka yi a shekarar 2014, sai kuma taron tunawa da babban wanda ya ba wa adabi gudunmawa, wato Dakta Abubakar Imam, mun yi taron a shekarar 2017, wanda shi Baba Mahmoon ya jagoranta.

Zauren taron ya cika maƙil

“Mu ‘ya’yan wannan ƙungiya mu na girmama yadda Baba Mahmoon ya riƙe mu cikin aminci da gaskiya da jajircewa.”

Daga ƙarshe, ta ce, “Bayan iyalan Baba-Ahmed, ya bar Alƙalam a bayan ƙasa. Kuma in-sha Allahu za mu ci-gaba da yin irin waɗannan tarurrukan domin tunawa da shi.”

Sannan ta yi godiya ta musamman ga dukkan mahalarta taron da kuma waɗanda su ka ba da gudunmawar gudanar da taron.

Haka shi ma Daraktan Shiyyar Kaduna na Hukumar Gidajen Rediyo Tarayyar Nijeriya (FRCN), Alhaji Buhari Auwalu, ya yi jawabi a matsayin sa na babban baƙo mai jawabi a wurin taron. Ya yi jawabin a kan irin ayyukan marigayi Mahmoon a aikin jarida.

Alhaji Buhari ya bayyana cewar Mahmoon ya wakilci gidan rediyon a wasu jihohi, musamman Kano, inda ya yi fice. A ƙarshe ya riƙe muƙamin shugaban gidan Rediyon Jihar Kano, daga bisani kuma ya zama shugaban Hukumar Yaɗa Labarai ta Jihar Kaduna (KSMC).

Ya nuna yadda bayan Mahmoon ya yi ritaya, bai huta ba, domin ya riƙe muƙamai a DITV da Liberty, sannan ya kafa jaridar Sawaba, kuma ya rubuta littattafan adabi guda shida.

Ya yanke shi da cewa ɗan jarida ne mara tsoro, kuma ɗan gwagwarmaya wanda ke feɗe gaskiya komai ɗacin ta.

Ya yi masa addu’ar Allah ya jiƙan sa, tare da kira ga matasa da su yi koyi da kyawawan halayen sa.

Shaihun malamin adabi, Farfesa Adamu Ibrahim Malumfashi na Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya shi ne ya yi sharholiya kan littafan Mahmoon guda shida, wato ”Yar Halas’, ‘Uwani Reza’, ‘Ɗan Hausa’, da fassarar littattafai uku na mashahurin marubucin nan na Ingila wato William Shakespeare guda uku: Macbeth (‘Makau’), Julius Caesar (Jarmai Ziza’), da Romeo and Juliet (‘Habiba Ta Habibu’).

A cikin sharhin nasa, farfesan ya ce, “Marubucin ya nuna cewa bai tsaya a fage ɗaya ba, ya ma fito a matsayin mafassari. Ba kasafai ake samun mutane su na ɗaukar fagage da dama ba. Mahmoon dai ya ɗauka. Shi ne marubucin kan sa, kuma mafassari ne, kuma mafassarin littattafan da ake ganin cewa wanda zai tunkare su sai wane da wane.

“William Shakespeare, kamar yadda manazarta su ka sani a yau, musamman a wurin Turawa, babu wani fitaccen marubuci kamar William Shakespeare. Saboda haka Mahmoon ya tunkari wannan aiki, kuma ya yi wannan fassara a waƙe. Amma kowa ya sani yin wannan fassara da salo irin wanda William Shakeapeare ya tunkara lallai zai kawo matsaloli iri daban-daban. Kuma ga dukkan alamu marubucin a shirye ya ke.”

Farfesa Malumfashi ya ci gaba da cewa, “Idan har duniya, musamman ma dai Turawan Ingila, su na ganin ba shi da na biyu, to mu ma ya nuna duk abin da Shakespeare ya ke taƙama da shi, to shi ma ya iya.”

A cewar sa, Mahmoon fitaccen marubuci ne ta kowace fuska, ba kawai ɗan jarida ba. “Ƙila mutanen Kaduna sun fi sanin shi a matsayin ɗan jarida, amma mu ƙila a jami’a za mu fi yin alfahari da shi ne a matsayin marubuci, mafassari.”

Farfesan ya ƙarƙare gabatar da sharhin sa da cewa, “Duk wanda ya tashi ƙididdigar mutanen da su ka ba da gudunmawa a harshen Hausa a zamanin nan, idan ya fara da Mahmoon Baba-Ahmed, sai in ga ya yi daidai, domin ya ba da gudunmawa. Allah ya saka masa da alkhairi.”

Wani babban malamin a Jami’ar Ahmadu Bello, Dakta Yusuf Nadabo (Sarkin Tudun Nufawa, Kaduna), shi ne ya gabatar da littafin Mahmoon na ƙarshe, wato ‘Habiba Ta Habibu’. Kuma ma ya yi taƙaitaccen jawabi, inda ya taɓo kusancin sa da marigayin.

Fitaccen marubuci kuma shugaban ƙungiyar masu shirya finafinai ta Jihar Kano (MOPPAN), Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON, ya gabatar da bayani kan ayyukan Mahmoon na rediyo da talbijin inda aka sako muryar sa a rahoto da ya aika wa shirin Dandalin Siyasa na FRCN Kaduna a cikin 1982, da kuma hoton sa ya na gabatar da shirin talbijin a DITV.

Daga nan sai aka kira wasu sha’irai su ka gabatar da waƙoƙin ta’aziyya ga marigayin, wato Malam Garba Lawal Buruku da Malam Nafi’u. Da man faifan waƙar Malam Yahaya Makaho aka sakawa a amsa-kuwwar zauren taron.

A ɓangaren sanya albarka kuwa, waɗanda su ka yi jawabi sun haɗa da aminin Mahmoon, wato Malam Abdullahi Nuhu, da maiɗakin marigayi Mahmoon, Hajiya Mama Zainab, da babban ɗan marigayin, Malam Aminu Mahmoon. Sun yi bayani cikin alhini tare da yi masa addu’a da kuma gode wa mahalartan taron.

Daga nan kuma sai aka karrama marigayin da lambar yabo ta girmamawa, wanda ɗan sa Aminu ya karɓa, sai kuma wasu mata biyu ‘ya’yan ƙungiyar waɗanda su ka riga mu gidan gaskiya, wato Hajiya Amina Haske da Hajiya Fatima VC. Iyalan su su ka karɓi kyaututtukan.

Bayan nan ne aka saurari jawabin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Nuhu Bamalli, wanda Ɗanmakwayon Zazzau kuma Hakimin Gundumar Kawo ya wakilta, wato Alhaji Jibrin Magaji.

Sai kuma aka saurari jawabin Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, daga bakin wakilin ta, Mista M. Galadima.

Daga nan kuma sai aka shiga fagen ƙaddamar da littafin ‘Habiba Ta Habibu’.

A ƙarshe, an kira shugaban kwamitin shirya taron, Malam Ibrahim Sheme, ya yi jawabin godiya ga mahalarta taron.

Taron ya yi armashi. An tashi da misalin ƙarfe 3:35.

Wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ɗanmakwayon Zazzau, ya na gabatar da jawabi

Taron, wanda aka yi a Gidan Arewa, Kaduna, ya samu halartar manyan mutane, iyalan marigayi Mahmoon da ‘yan’uwan su na jini da iyalan marigayi Alhaji Abubakar Imam da membobin ƙungiyar Alƙalam, da kuma marubuta, ‘yan jarida da sauran ɗimbin jama’a daga sassa daban-daban.

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci taron sun haɗa da Alhaji Inuwa Jibrin, Alhaji Lawal Yusuf Saulawa, Alhaji Idris Jigo, Alhaji Ibrahim Balarabe Musa, Alhaji Ɗahiru Ahmad, Sir Falal Jalal, Hajiya A’ishatu Giɗaɗo Idris, Alhaji Mu’azu Nadabo Chanchangi, Hajiya Sadiya Kaduna, Malam Zakari Aminu, Malam Shafi’u Magaji Usman, Alhaji Shu’aibu Gimi, da wakilin tsohon shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Tarayya Mai Shari’a Umaru Abdullahi (Walin Hausa).

Haka kuma akwai Malam Shehu Mu’azu, Malam Al-Amin Abdullahi Albani, Malama Rahama Aminu Yakawada, da sauran su.

Su Dakta Yusuf Nadabo da Alhaji Buhari Auwalu a babban tebur
Dakta Yusuf Nadabo Abdullahi ya na gabatar da jawabi
Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya na gabatar da jawabi
Tarin littattafan Mahmoon Baba-Ahmed
Alhaji Aminu Mahmoon Baba-Ahmed ya karɓi kyautar karrama mahaifin sa
‘Ya’yan memba ɗin Alƙalam, marigayiya Hajiya Amina Haske, su na karɓar kyautar karramawar da aka yi wa mahaifiyar su

Leave a Reply