Labarai

ƊAN TAKARAR SANATA A JAM’IYAR APC MAI MULKI YA RASU A ASIBITI A BIRNIN SIN WATO CHINA.

 

Ɗan takarar kujerar Sanata mai wakiltar Jigawa ta Kudu maso yamma na jam’iyyar APC, Honorabul Tijjani Ibrahim ya rasu.

Ya rasu ne a ranar Asabar 13 ga watan Agusta a wani asibitin kasar Sin.

Ibrahim, wanda tsohon ɗan majalisar wakilai ne, an ce an kwantar da shi a wani asibitin Abuja domin jinyar ciwon hunhu daga inda aka garzaya da shi ƙasar China domin ci gaba da kula da lafiyarsa a lokacin da yanayinsa ya tabarbare.

Ibrahim ya rasu ne watanni uku bayan ya lashe tikitin takarar Sanata na jam’iyyar APC a shiyyar sa inda ya samu kuri’u 361.

Da yake tabbatar da rahoton, Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru, a cikin sakon ta’aziyyarsa ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Habibu Kila, ya ce rasuwar Mista Ibrahim “babban rashi ne ba ga iyalansa kaɗai ba har ma ga al’ummar Musulmi”.

Gwamna Badaru a cikin sanarwar ya bayyana Mista Ibrahim a matsayin Ɗan siyasa mai aminci kuma mai dogaro da shi wanda ya ba da gudummawa sosai ga ci gaban siyasar kasar.”

Ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya ba shi ni ima dawwamamme, ya kuma baiwa iyalansa haƙurin jure rashin.

Marigayi Ibrahim ɗan siyasa ya wakilci mazabar Dutse/Kiyawa tarayya a majalisar wakilai tsakanin 2011 zuwa 2015.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button