Yadda TIGMEIN Take Shirin Yin Gagarumin Bikin Bayar da Tallafi ga Mutane Ɗari Biyar Mata da Maza na Jihar Kano Musamman Mabiya Ɗariqar Tijjaniya

0
93

 

Daga Bilkisu Yusuf Ali

Ƙungiyar Tijjaniya Grassroots Mobilization And Empowerment Initiative of Nigeria (TIGMAIN) reshen jihar Kano, Ta kira taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki na ƙungiyar ranar 6/11/2022 a Unguwar Kurna da ke jihar Kano. Taron an tattauna hanyoyin da za a bi don tabbatuwar wannan qudirin na bayar da tallafi maza da mata, kuma tallafin mai tsoka ga mutum ɗari biyar na jihar Kano waɗanda suka fito daga ƙananan hukumomi arba’in da huɗu.

Shugaban riƙo na Kano Injiniya malam Rabiu Fansheka shi ya jagoranci wannan zaman.Daga cikin shirye-shiryen da ake son a gabatar a ranar akwai ƙaddamar da shuwagabannin ƙungiyar na jihar. sannan aka An tsara za a gudanar da wannan tallafi ne ga al’ummar jihar Kano don sanya al’umma su dogara da kansu , su taimaki kansu. A tsarin wannan tallafin za a koyar da sana’oi da daman gaske waɗanda suka shafi mata da maza sannan a tallafawa waɗanda suka koyi wannan sana’ar da jarin ci gaba da gudanar da sana’ar.

A irin wannan lokacin ya zama wajibin al’umma duk wanda yake da hali ko yake da ilimin wata sana’a ko hanyar koyon wata sana’a da ya bayar da haɗin kai don al’umma ta ƙaru saboda fita daga wannan matsatsi da al’umma ke fuskanta a yau. Shugaban ƙungiyar na riqon kwaryar na jihar Kano ya kuma yaba wa ‘yan ƙungiyar na jihar Kano bisa aikin da suke yi ba dare ba rana don tattaro ‘yan ɗariqar Tijjaniya da zawiyoyi saƙo da lungu birni da ƙauye na jihar Kano da fito da su don a samu haɗin kai da taimakekeniya tsakanin juna da zama inuwa guda. Haƙiƙa iya wannan kaɗai babbar nasara ce a tafiyar TIGMEIN. Ƙungiyar TIGMEIN ƙungiya ce ta ƙasa kuma ta haɗin kan mabiya ɗariƙar Tijjaniya na kowanne

ɓangare na kowacce zawiyya ba tare da kowanne irin ɓangaranci ba, a faɗin ƙasar nan don gudu tare a tsira tare.

Shehi Ahmad Tijjani Sani Auwal Shugaban TIGMEN na Kasa.

Tuni ire-iren wannan tallafin da haɗin kai

ya yi nisa a wasu jihohin a ƙasar nan , inda su sun jima da amfana da wannan hangen nesan na shugaban wannan ƙungiyar na ƙasa Shehu Tijjani Sani Auwalu wanda jika ne ga Shehi Ibrahim Niasss. Inda wasu jihohin har an fara kakkafa masana’antu a ƙarƙashin wannan ƙungiya wanda ‘yan ɗariqar Tijjaniya da ma waɗanda ba ‘yan ɗariƙar ba suna nan suna ta amfana da san-barka. Taron ya samu halarta coordinator s na Kano ta Arewa da Kano ta tsaliya da kano ta kudu. Kuma kowanne daga cikinsu ya kawo cigaban da aka samu a ɓangarensa.

Leave a Reply