‘Yan ta’addar Boko Haram sun kashe wasu mata 15 da su ke zargin su da yin asiri a Borno

0
62

Daga Wakilin mu

‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe wasu mata 15 da suka zarga da yin asiri a jihar Borno. Majiyar soja ta ce lamarin ya faru ne a tsaunin Mandara da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar.

Jaridar Punch ta bayyana cewa, Ali Ngulde, kwamandan Boko Haram mai kula da tsaunin Mandara, yankin Gwoza, da wasu sassan ƙasar Kamaru, ana zargin shi ne ya bayar da umarnin yanka waɗanda aka kashe. Ya ce, “Labarin da kuka ji cewa sun kashe mata 20 ba gaskiya ba ne; sun kashe mutane 15, kuma su mambobinsu ne; sun kashe su ne kwanaki huɗu da suka wuce.

“10 daga cikin matan ‘yan ta’addan ne suka kashe su bayan sun zarge su da maita yayin da aka kashe wasu mata biyar saboda yunƙurin miƙa wuya ga sojoji.
“Shugaban Boko Haram mai kula da tsaunin Mandara, Gwoza General Area, da wasu sassan Kamaru,

Ali Ngulde, ya bayar da umarnin kashe su,” in ji majiyar. Tare da samun nasarar kai hare-haren bama-bamai ta sama da aikin share fage a dajin Sambisa, Gaizuwa, da kuma tsaunin Mandara a cikin kananan hukumomin Bama da Gwoza. Mayaƙan Boko Haram dai da dama suna ta miƙa wuya ga sojoji.

Leave a Reply