“Yara 100 ne ke mutuwa duk sa’a a Najeriya saboda rashin abinci mai gina jiki” a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya (UN)

0
22

Daga Abu Usaimin

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce Najeriya na asarar kimanin yara 100 a cikin sa’a guda sakamakon rashin abinci mai gina jiki wanda ke nufin kusan mutane 2,400 ke mutuwa a kullum.

Babban jami’in kula da abinci na UNICEF a Najeriya Nemat Hajeebhoy ne ya bayyana hakan a lokacin da yake magana a Legas a yayin wata tattaunawa da shugabannin kafafen yaɗa labarai.

Majalisar kula da abinci ta kasa ce ta shirya taron wanda mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta. Hajeebhoy ya bayyana cewa Najeriya na fuskantar matsalar abinci mai gina jiki ta gaggawa kuma ya yi kira da a ƙara samar da kuɗaɗe da sauran matakan da za su taimaka wajen magance ƙalubalen cikin gaggawa.

Ta ce kashi ɗaya bisa uku na yara a Najeriya na fama da matsanancin talauci na abinci, sannan kuma a kwanaki 1,000 na farko na rayuwar yaro na ba da dama ta musamman wurin daƙile matsalar rashin abinci mai gina jiki da illolinsa.

“Rashin cin abinci mara kyau yana hana miliyoyin yara kiwon lafiya, ci gabansu da kuma rayuwarsu, domin a kowace sa’a, yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar kusan 100 ne ke mutuwa a Najeriya. Idan ba a kula da su ba, yaran da ke da matsanancin rashin abinci mai gina jiki sun fi mutuwa kusan sau 12 fiye da yaro mai lafiya.

“Najeriya ce ta daya a Afirka kuma ta biyu a duniya a fannin yara masu fama da tamowa. Wannan ba irin ƙididdigar da ya kamata mu yi alfahari da ita ba ce, ba tare da ɗaukar matakin gaggawa ba, UNICEF ta kiyasta cewa kimanin yara miliyan 14.7 ‘yan ƙasa da shekaru biyar za su yi fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki a bana.

Nijeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar kare hakkin yara a 1991 kuma samun abinci mai gina jiki muhimmin haƙƙi ne na kowane yaro.

A shekarar 2003, Najeriya ta rattaba hannu kan dokar kare haƙƙin yara kuma jihohi 29 cikin 36 na da dokar kare haƙƙin yara.”

“dan muna da waɗannan duka, me muke yi game da ‘yancin waɗannan yara miliyan 21 na samun abinci mai kyau?” Ta tambaya. Ta yi nuni da cewa, kuɗin da ake kashewa wajen magance kalubalen shi ne asarar kashi 15 cikin 100 na jimlar kayayyakin cikin gida ga Najeriya.

Hajeebhoy ya bayyana cewa, abincin da ake amfani da shi na makamashi kaɗai yakan kai Naira 707 ga kowane gida a kowace rana yayin da abinci mai gina jiki ya kan kai Naira 1,687 a kowace rana, wanda kashi 34 cikin 100 na gidaje a ƙasar nan ba sa iya biya.

Babbar mataimakiyar shugaban ƙasa ta musamman kan abinci mai gina jiki, Misis Abimbola Adesanmi, ta ce taron na da nufin ƙara wayar da kan jama’a game da matsalar rashin abinci mai gina jiki da wayar da kan ‘yan ƙasa a matsayinsu na masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply