YARA MAYAN GOBE.

0
67

YARA.

Rayuwar yaro koma wanne irin Jinsi ne Walau Mace Ko Namiji abar ƙauna ce abar so ce sannan kuma ado ce wadda take cike da nishaɗi da walwala da kuma jin daɗi.

Shiyasa zaka ga duk wanda Allah ya azurta da haihuwar yara a kullum yana cikin farin ciki da walwala sannan kuma bazai taɓa zama cikin kaɗaici ba.

Haka zalika duk gidan da Allah ya nufa da yara ya wuce a kirashi da kango
haka zalika ko da a cikin Malaman Makaranta duk Malamin da yake tare da yara zaka ga kwakwalwarsa tafi aiki sannan kuma ya na da tarin ilimi tun daga na karatu har zuwa kan na iya rayuwa da Dan Adam.

A duk lokacin da akaga Magidanci da yara sai kaga a na taya shi murna a na sha’awarsa.

Ko a lokutan bukukuwan sallah duk lokacin da Magidanci ya fito da yaransa zashi masallaci sai kaji jama’a suna ta sa albarka.

Rayuwar yara tana cike da darrusan da duk wanda ya ma’amalantu dasu zai kasance mai ilimin zama da mutane wato SOCIOLOGY.

Yara manyan gobe.

Leave a Reply