Daga wakilinmu
Daga jahar Gombe yarinya mai suna Fatima Adamu Maikusa, ta kafa tarihin lambobin yabo na duniya har guda 7 a ilimin lissafi.
Fatima Adamu Maikusa wadda ta kasance ‘yar baiwa daga jahar Gomben Najeriya, ta lashe lambobin yabo
mabambanta guda 7 a faɗin duniya. Wannan ya sa ta kafa tarihin zama ta farko a Najeriya da ta lashe wannan kambu.
Tun Fatima na da shekara 9 ta fara nuna hazaƙa, kuma ta zama madubin dubawa ga sauran yara mata.
A yanzu haka tana matakin na 11 a makarantar Nigerian Turkish International School (NTIS) da ke Kano.
Gasannin da Fatima ta lashe akwai American Mathematics Competition (AMC), International Eduversal Mathematics Competition a Jakarta da Indonesia. Da wasu gasanni a Bangkok, Thailand and Kangouro Sans.
Sannan akwai gasar Future Intelligence Student Olympiad (FIOS), Mathematics Without Borders a Bulgaria sai kuma Komodo Festival a Indonesia.