Hirarraki

Dikko Radda Mutum ne mai tausayin mata:Hajiya Zulaiha Dikko Radda

 

Dr Dikko Umar Radda ya yi alqawarin  bai wa mata a jihar Katsina ingantaccen ilimi da sana’oin da za su dogara da kansu su tallafi iyalansu da ba su dama a madafun iko da tafiya tare da su don inganta rayuwarsu da ciyar da jihar Katsina gaba. Ta bakin maiɗakinsa Hajiya Zulaiha Dikko Radda

Za mu so mu ji taqaitacce tarihinki?

Ni sunan Hajiya Zulaiha Abdullahi Matazu mahaifina ɗan Matazu ne mahaifiyata ‘yar Dutsim-ma. An haife mu a Kaduna a nan muka tashi. mahaifnmu mai kishin jihar Katsina ne sosai ,saboda haka da lokacin da muka isa shiga Sakandire sai ya dawo da mu gida Katsina.Na yi sakandire a GASS Kabomo. Na fara 1996 na kammala 2001.Bayan na kammalaa an yi min aure a shekarar 2001 . Muna da yara guda 7.

Maigidana Alh Dikko Umar Radda mutum ne mai kishin karatun mata don haka bayan mun yi aure ya yarje min na ci gaba da karatu. Na fara Difloma a ɓangaren shari’a (law) a nan Aminu Kano collefe of Legal studies a Kano.

Da na gama law sai ya kasance kuma mahaifina bai ba ni qarfin gwiwa ba a fannin shari’a ba, saboda yana cewa duk alƙalancin da za a yi. ba a kan alƙur’ani da sunna ba, to mutum wuta zai je.
Wannan yasa na sauya ɓangare na koma BUK inda na yi advance difloma a public administration.

Da na gama sai suka ba ni admission inda na yi Bsc a political science . Bayan da maigidana ya samu sauyin aiki a SMEDAN sai na koma jami’ar Gwagwalada da ke Abuja na yi digirina na biyu a public administration. Alhamdlillah

A matsayinki na matar ɗan takarar gwamnan jihar Katsina wanne fata za kiyi da tanadi ga mata a alƙawurwura da ki ke yi a wannan zagayen na neman su zaɓi Maigidanki?

Dr Dikko Radda mutum ne da yake da tausayin mata. Yana son ya ga mata cikin walwala ba ya son ya gansu da wahala duk wanda yake mu’amala da shi yau da gobe zai yi shaidar hakan. Ko kan hanya yake tafiya indai zai ga mace da kaya a kanta to kuwa da kansa zai karɓa ya taimaka mata.
Kullum yana cewa mata masu rauni ne ya kamata a tallafe su. Kin ga mai wannan tausayin ba yadda zai yi ya bar mata a wani hali na rahin jin ƙai.Haka duk inda ya ga mace mai rauni sai ya tallafa mata.

Alhamdlillah ko a lokacin yana SMEDAN mata su suka fi alfanar tallafinsa saboda ya lura sune suke da rauni kuma sune in an tallafesu taimakon yake tafiya kai tsaye ga iyalansu.

Dr Dikko mutum ne da yake son ganin mace ta tsaya da ƙafafunta don haka yake tsaye kan ilimin mata da ba su sana’a kuma na tabbata da Allah ya ba mu nasara a wannan mulkin zai bayar da gagarumar gudummawa a wannan ɓangaren.

Don haka nima zan yi iyakar ƙoƙarina na ga na ba shi haɗin kai da tallafa masa ta ɓangarena don tabbatar da wannan ƙudirin nasa. Nima kuma ba wai zan zauna ba ne zan yi amfani da duk iyakar iyawata bisa hurumin da doka ta bayar na ga na tallafi matan nan musamman ma ta ɓangaren sana’a.

Wadda take da sana’a za mu ƙarfafeta wadda muka tabbatar ta iya za mu ba ta dama ta koyawa wasu wannan sana’ar wannan shi zai qara tallafarta. Waɗanda kuma ba su iya ba, su ma anan zai sa su koya sannan za mu ba wa duk wanda ya koya jaro don ci gaba da tafiyar da sana’ar.
Haka a bangaren neman ilimi nan ma za mu tallafawa mata sosai saboda duk wani cigaba yana ƙarƙashin ilimi.

In uwa ta kasance mai ilimi za a tarar da ‘ya’yanta a nutse kuma za ta tsaya gun tarbiyya da ilmantar da ‘ya’yanta a gaba.
A jihar Katsina akwai mata da aka kashe mazajensu ko aka raba su da muhallansu wanne tanadi ku ka yi musu?

Alhamdlillah maganar rashin tsaro mu mun je mun zagaya mun ga abubuwa da kanmu mun ga tashin hankali. A irin wannan rayuwar duk wahalar kan koma kan mata ne.

Su suka fi shiga ruɗanin kuma kada ki manta ciwon ‘ya mace na ‘ya mace.
Wani gida da na je lokacin da matan ke ba ni laɓarin abin da ya faru ban san lokacin da na ga ina hawaye ba.

A bin tausayin wasu mazajen an kashe su. wasu matan ma ba su da tabbacin mazajen suna raye ko ba sa rayen. wasu ma a gabansu aka yi wa mazajen mugun kisa, ko uwa a gabnta a kashe xanta tana gani.

Wannan abu ne marar daɗi da ya kamata a duba kuma muna nan da burin tallafar ire-iren waɗannan za mu dau nauyin karatunsu mu ba su ayyukan yi don dai su zo su tallafi iyalansu, ba za mu bari su shiga wani hali ba da yardar Allah.

Sannan muna addu’a kan wannan rashin zaman lafiyar kuma abin da Dr Umar Radda zai fi mayar da hankali akai fatansa kowa ya koma inda yake a ci gaba da walwala da kwanciyar hankali in sha Allah da addu;a da taimakon Allah da jajircewa, Sabida mata duk inda aka je aka dawo kan mata abin yake ƙarewa.

Ya batun ilimi wanne alqawari ku ka yi a wannan vangaren?

Abu ba farko da Maigidana na ya yi alƙawari shi ne samar da ingantaccen ilimi musamman mata da matasa waɗannan sune za su ci gajiyar wannan hoɓbasa da Dr Dikko ya yi. zai ɗauki malaman makaranta a koya musu sababbin hanyoyi na koyar , za a yi musu training a matakai daban-daban. , malaman kuma za a ware lokaci da za’ayi musu bita ta musamman don su samar da ilimi ingantacce.

Batun lafiya fa tunda lafiya uwar jiki?
Batun kiwon lafiya da duba mata masu ciki da shayarwa duk mun yi alƙawari za mu ke bayar da magani kyauta. Fatanmu yin komai cikin farin ciki da ikhlasi don samar da al’umma lfiyayyiya ingantacciya.

Me ne ƙalubalenki musamman wanda ki ka gani da idonki a zagayen da ki ke yi?
Ƙalubalenki shi ne yadda na ga mata babu abin yi sannan babu wadataccen ilimi sannan mata na kuka da yadda ba a cika musu alqawarurruka bayan zave. Wanda na yi musu alqawarin wannan matsala ta kau.
Duk da ba a mugun sarki sai mugun Bafade to in sha Allah za mu sa ido sannan za mu ɗau mataki don tabbatar da wannan ƙalubalen da na gani ya kau.

Wanne Kira za ki yi wa mata kan fita zaɓe?
Babban kira na shi ne don Allah mata ku fita ku je ku karɓo katinan zaɓenku. Katinan nan da su , naku ne , birjik a ma’aikatar zaɓe.

Zaɓen nan na mata ‘yancinmu ne. Mu mata an san mu da alqawari sannan an sanmu da tunani da kaifin basira don haka mu karɓo kayanmu sannan ranar zaɓe mu yi haƙuri mu jure mu kaɗa Ƙuri’a kuma mu zaɓi APC daga ƙasa har sama nasara tamu ce da yardar Allah.

Wannan kiran ba iya mata ba ne har da mazan. Wanda kuskure ne .duk inda ka ke son mutum in har ba ka da katin zaɓe ba yadda za ka zaɓe shi, Kuma dai ka tuna sai ka yi zaɓen ne burinka akansa zai cika, Ka tuna da ƙuri’arka ɗaya za ka iya tabbatar da kujera.

Kuma wannan kujerar in ka yi dacenta ko ba ka da rai wani naka zai amfana tunda an zaɓi mutum na gari.
Don haka a je a karvi katin zaɓe kafin a rufe, Sannan mata su daure sati biyu kafin zaɓe kada su yi lalle saboda yatsunsu na’urar ta gan shi.

Hajiya Zulaiha Dikko Radda mai ɗakin ɗan takarar. Gwamna a jjam”gyara APC a jihar Katsina

Ana raɗe–raɗin kuna sayen katunan zaɓe ?

Wannan magana ƙarya ce kuma jita-jita. Ai an kama waɗanda suke yi an kuma kai su ga hukuma. Ba ma yi ba mu tava sanyawa ba, Don haka ma maigirma ɗan takarar Gwamna a jam’iyyar APC Dr Dikko Umar Radda ya ce “duk wanda aka gani da katunan zaɓe ba bisa qa’ida ba a yi rahotonsa ga ‘yansanda kuma a kai shi kotu da aka tanada musamman don wannan laifin”.

Ai mu Alhadlillah, mu muna da imanin cewa a wurin Allah muke nema sannan al’ummar jihar Katsina mutane ne wayayyu da suka san cancanta kuma zaven cancanta za su yi. Ba su da wanda ya fi Dr Dikko Umar Radda cancanta.

Sannan muna son komai za mu yi mu yi shi da ikhlasi da tsoron Allah don haka in ka sayi kuri’a ai ka yi ha’inci, duk abu na ha’inci ba za ka samu Dr Dikko a ciki ba.

Fatanki ga al’ummar jihar Katsina?

Babban fatana shi ne a yi zaɓe lafiya a kammala lafiya , sannan ranar zaɓe a yi jam’iyyar APC daga sama har ƙasa. Mata da maza su fito su rama karamci da karamci.
Na gode.

Leave a Reply

Back to top button